
Sau da yawa mutanen mu basu jin labarin coins masu kyau sai lamarin su yayi nisa, mutanen mu sukan so ace sun samu tokens din da zasu yi musu times 50 (×50) ko ×100 ko sama da haka, amma galibi sai token yayi times da yawa labarin sa yake zuwa, misali BOME, WIFF, BONK, Shiba, Slert da sauran su.
~ Idan mutane suna so su zama independent wato su samu 'yanci ba sai sun dogara da wani ya kawo musu bayani ba, kai da kanka zaka iya samo token da zai maka ×10 ko ×100, amma sai kabi wasu hanyoyi guda 8 a ƙalla kenan, idan sabbin Coins ko tokens kake nema.
1. Ya kamata mu 'kara fahimtar cewa komai yana zagawa ne akan Liquidity, duk abinda zai je ya dawo toh Liquidity shine farko.
~ Wato Dala Miliyan nawa ne a cikin coin din? Dala dubu nawa ne a cikin sa? da Dala nawa token din ya fara? dole ka gano wannan a karon farko.
2. Na biyu, dole ka dinga aiki da kayan aiki (Tools) dole ya zama kana da:
1. DEX Screener.
2. DEX Tools.
3. Birdseye.
~ Dazu munyi magana akan Coin Gecko da Coin Market Cap da Coin Carp a Sihaad Telegram, ba sai mun sake ba a nan.
Amma in kana son yin trading me kyau a cikin sabbin tokens 'yan yayi, a karon farko da bayyanar su toh ka mallaki DEX Screener, DEX Tools, da irin su Birdseye da sauran su.
Idan muna magana akan sabbin tokens kenan wadanda galibi kan DEX ake fara launching dinsu, a galibin lokuta sai an gama cin moriyar su sai kaji ance za'a kaisu CEX.
~ Idan ka dauki DEX Screener, zaka ga wajen Chains, wato Blockchains, zaka zabi Chain din da kake so kaga sabbin Coins akan ta.
Misali, sai in zabi BASE Blockchain, toh zanyi ta ganin sabbin tokens da ake deploying dinsu yanzu yanzu akan BASE Blockchain idan na saka Sort din akan New. Idan ka so sai ka zabi All Chains, zai zubo maka tokens na kowane Blockchain da DEX Screener din take fetching data akan sa. Amma idan kaji labarin cewa yanzu anfi samun kuɗi akan Blockchain kaza toh ka zaɓe akan Dex screener.
~ Misali, a yanzu haka kudaden suna juyawa daga kan Solana suna komawa kan BASE.
Bayan kayi settings Blockchain din da kake son ganin sabbin tokens dinsu:
~ Sai ka lura da time din da aka fara trading na token din, da kuma yawan kuɗin da yake cikin sa, Market Cap, da trading din da ake yi, shin selling ko buying wanne yafi yawa?
4. Su wanene top holders? shin akwai wasu wallets din da suke rike da coins din da yawan gaske? idan akwai toh akwai Matsala kenan, domin wallet daya idan ta siyar zata iya jijjiga kowa, zata iya jefar da mutane kasa.
~ Sannan anyi renouncing contract din? shin Liquidity din an kulle shi? tsawon yaushe aka kulle? shekaru nawa?
Duk zaka samu wadannan bayanan akan DEX Screener, daga nan ne zaka yanke hukuncin me zaka yi.
~ Idan ka gamsu zaka saya, sai ka duba kaga a wace kasuwa ta DEX za'a samu token din, idan Solana ne toh dayan uku, ko Raydium, Jupiter ko Kamino, idan BSC ne irin us Pancake Swap, ko UNISWAP idan Ethereum ne.
~ Ko Archer swap, LFG, BOW Swap, ICE Cream swap, Shadow swap idan CORE ne.
Sai ka duba da me ake saya?
Ethereum, BNB, CORE ko wrapped token dinsu? sai kaje ka nemo ka saya. Dukkan wadannan bayanan zaka gansu akan su DEX Tools da DEX Screener da sauran Token Data Aggregators.
5. Sai ka koma kabi su a Twitter (X) me suke cewa? menene mutane suke cewa akan project din, shin suna da Website? je ka duba, me suka rubuta, shin abinda suka rubuta zai yiwu ayi achieving dinsa a hankalce?
~ Misali sai kaga token din yana da 1 Billion supply, sai kaji sunce zuwa karshen wata coin su zai kai Dala 10 ko 20, wannan ba abu ne me yiwuwa ga Meme ko Shitcoins ba.
6. Sannan ka dawo ka duba inflow, kudaden da suke shiga cikin token din, misali, da karfe 7 na safe Market Cap dinsa yana 1 million Dollars, karfe 7 da minti 20 ya karu zuwa 1.3 kaga an samu karin Dala dubu 300 a cikin minti 20.
~ Wannan duk zai taimaka maka wajen yanke hukuncin ka shiga ko karka shiga, in zaka shiga da Dala nawa zaka shiga, sannan for how Long zaka zauna a cikin token din idan ka saya.
7. Low Caps:
Ka bayar da muhimmanci wa tokens din da suke da karancin Market Cap, kudin dake cikin su kadan ne, misali sai kaga wani Coin suna da Twitter, suna da Telegram, suna da Website, suna bayanai cikin nutsuwa da kwanciyar hankali, sannan basu dade da launching token dinsu ba, sannan kudin dake cikin sa kadan ne.
~ To ka bayar da muhimmanci ma irin wannan. Idan kaga coin yana da manyan kudade a cikin sa toh da wahala yazo yayi wani abun kirki a kusa kusa, alama ce da take nuna an sanshi, anci moriyar sa tun kafin kazo.
8. Sannan bayan ka kammala binciken ka, duk kyan coin karka zuba masa kudi masu yawa, abinda nake nufi da kudi masu yawa shine a wajen ka, domin kowa da matsayin sa. Misali idan nace kadan ina nufin kudin da a zuciyar ka a wajen ka 'yan kadan ne.
~ Misalin, a wajen babban influencer Dala 100 kudi ne yan kadan, koda sun lalace ko a jikin sa, zai ce oho, wani a wajen sa kudi kadan sune Dala 5 ko Dala 10.
Idan ka zuba Kudi kadan kamar Dala 10 sai kaga ta dawo 30 toh kaje ka cire 15, kaga ka dawo da uwar kudin ka tare da ribar Dala 5, sannan still kana da investment na Dala 15 a ciki.
~ Kar ka yarda tashin Coins din ya rude ka kaje ka dauko wasu kudin ka kara a ciki, saboda sabon Coin ne, sabon token ne, ba'a gama sanin halin Developers dinsa ba. (Gara ace ba'a ci kasuwa da kai ba akan azo ana cewa an fadi tare da kai), wannan Market formula ce ka rike ta da kyau.
9. Na karshe duk research dinka ka dinga mayar da komai a hannun Allah, yana daga cikin abinda yasa mutane suke faduwa a trading duk da cewa sunyi research shine basu jingina abubuwan zuwa ga ikon Ubangiji.
~ Shiyasa Allah yake barin mu da research dinmu, sai muyi ya faduwa, idan kayi research sai kayi addu'a, ka fadawa Allah cewa kai ba kowa bane, amma kayi abinda zaka iya na bincike, Allah ka fitar damu.
Idan kana yin haka da wahala Allah ya bari kaji kunya ko fadi.
Rubutu na farko kenan, a na biyu zamu tabo wasu Tools, kayan aiki da ake iya gano sirrin tokens, da abinda aka boye wanda idan ba da binciken kwakwaf ba toh ba za'a san dasu ba.
~ Sannan dole mutane su rage lalaci, wadannan aiyukan suna da wahala, suna cin lokaci, haka ake zama independent, idan baku tashi kuka zama independent ba za kuyi ta wahala ne ana wasa da hankalin ku, kuna pumping coins ana zare kudi ana barin ku da lambobi.